Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Kwamitin tsare-tsare na kudi (MPC) na Babban Bankin Najeriya (CBN), ya daga darajar lamuni a kasar da maki 150 zuwa kashi 26.25 cikin dari.
Mista Yemi Cardoso, Gwamnan CBN ya bayyana haka ne ranar Talata a Abuja, yayin da yake karanta sanarwar taron MPC karo na 295.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin jihar Kano ta kaddamar da gyaran dokar masarautu
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wannan shi ne karo na uku a jere na tsaurara matakan bayar da lamuni, wanda aka fi sani da Monetary Policy Rate (MPR) na MPC karkashin Cardoso.
Cikakken bayanin na tafe…