Kwamitin bincike na gwamnatin tarayya ya tuhumi jami’an gidajen gyaran hali kan cin hanci da take hakkin dan adam

1001230545 750x430

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin hukunta jami’an gidajen gyaran hali da kwamitin bincike ya kama da laifin cin hanci, amfani da iko ba daidai ba, da kuma take hakkin bil’adama.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, inda aka gabatar da rahoton kwamitin binciken kan zarge-zargen rashin da’a a cikin hukumar gidajen gyaran hali ta kasa.

Ya ce jami’an da aka samu da laifi za su fuskanci hukunci na ladabtarwa da kuma shari’a bisa dokokin da ke aiki, yana mai jaddada manufar rashin jurewa cin hanci da duk wani nau’i na take hakkin bil’adama.

Ya kara da cewa gidajen tsarewa ba wuraren azabtarwa ba ne, illa cibiyoyi ne na gyara hali da sake mayar da mutane cikin al’umma, domin duk wanda ke tsare yana da mutuncinsa da hakkinsa na dan adam.

Ministan ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne bayan samun manyan zarge-zarge na rashin da’a da suka hada da cin hanci, amfani da iko ba daidai ba, azabtarwa da wulakanta fursunoni.

Ya ce binciken na da matukar muhimmanci wajen dawo da gaskiya da inganta sahihancin hukumomi, yana mai yabawa mambobin kwamitin kan kokarinsu.

Babban kwanturola janar na gidajen gyaran hali, Sylvester Nwakuche, ya bayyana wannan mataki a matsayin wata dama ta duba kai da gyara, yana mai cewa dole ne a dauki mataki mai karfi tare da kare martabar jami’an da ke aiki da gaskiya.

Ya kara da cewa mataki na gaba zai mayar da hankali ne kan aiwatar da gyare-gyare da suka hada da inganta jin dadin ma’aikata, horaswa, da kuma daidaita aiki da ka’idojin kasa da kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here