Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027 da su yi murabus daga mukamansu, bisa tanadin dokar zaɓe.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an isar da wannan umarni ne ta wata takardar gwamnati da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya fitar, inda aka bayyana muhimmancin bin dokokin da ke jagorantar yadda jami’an gwamnati ke gudanar da harkokinsu.
Takardar ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da sashe na 88 (1) na dokar zaɓe ta shekarar 2026, wanda ke tsara yadda masu riƙe da muƙaman gwamnati za su shiga harkokin siyasa.
Ta ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da rashin son kai, gaskiya da riƙon amana a cikin aikin gwamnati, tare da samar da daidaito ga duk masu neman takara.
A cewar takardar, duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓen mai zuwa dole ne su yi murabus ko ritaya, gwargwadon hali, kafin ko a ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026.
Haka kuma, an umarci dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomi na gwamnati da su yaɗa wannan sanarwa sosai tare da tabbatar da cikakken bin umarnin.











































