‘Yan ta’adda sun sace mutane 22 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sa’o’i bayan ziyarar IGP

Abuja Kaduna highway
Abuja Kaduna highway

‘Yan ta’adda sun kai farmaki wasu gidaje a Anguwar Maji a garin Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka yi awon gaba da mutane 22.

Hakan dai ya faru ne sa’o’i 24 bayan da babban sufeton ‘yan sanda na kasa (IGP), Usman Alkali Baba ya ziyarci babbar hanyar.

Garin Jere, wanda ke da iyaka da Tafa-Sabon-Wuse a Jihar Neja, yana kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wani mazaunin Unguwar Maji mai suna Shehu Bala, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin na baya-bayan nan ta hanyar tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi.

Ya ce ‘yan bindigar da suka zo da yawa sun mamaye wasu gidaje inda suka yi awon gaba da mutane 22 ciki har da mata biyar.

“’Yan bindigar sun zo da adadi mai yawa yayin da wasunsu ke sanye da kakin sojoji.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun shafe sama da awa daya suna gudanar da ayyukansu cikin natsuwa a cikin al’umma.

Ya kara da cewa sun fara harbe-harbe ne kawai don tsoratar da mutane daga bin su bayan sun bar al’umma.

Bala, ya ce daya daga cikin mutane 22 da aka yi garkuwa da su ya tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi yayin da ake kai su cikin daji.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here