Hukumar INEC ta karbi wasika daga mazabu na sake kiran dan majalisar wakilai

Majalisar, Tarayya, Najeriya, mazabar, jihar, zamfara, Hukumar, INEC, wakilai, karbi
Mazabar Kaura Namoda-Birnin Magaji ta jihar Zamfara sun sanar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu kan kudirinsu na...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Mazabar Kaura Namoda-Birnin Magaji ta jihar Zamfara sun sanar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu kan kudirinsu na kiran Hon. Aminu Sani Jaji daga majalisar wakilai.

Al’ummar mazabar sun ce sun yanke hukuncin ne saboda rashin samun wakilci kamar yadda sashe na 69 na kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Karin labari: Wasu ‘yan ta’addar ISWAP sun kashe DPO tare da raunata mutum 2 a Borno

Wasikar sake kiran da ‘yan mazabar suka mika wa ofishin shugaban hukumar da ke hedikwatar INEC a Abuja, an amince da shi da kuma buga tambari.

Mazabar sun kuma fara tattara sa hannun masu kada kuri’a kamar yadda yake kunshe a cikin rajistar masu kada kuri’a, inda za a mika wa hukumar domin tantance sa hannun masu kada kuri’a sannan kuma za ta gudanar da kuri’ar raba gardama don kiran Jaji.

Karin labari: Yanzu-yanzu: CBN ya umarci OPay da Moniepoint da sauransu da su cigaba da karbar kwastomomi na dan lokaci

Sanarwar mai dauke da sa hannun Hon. Bello Mahmud Birnin Magaji, shugaban Coalition for Sustainable Democracy da sakatarenta, Kwamared Mustapha Ibrahim, ya ce, “Muna kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a a mazabar da su fito baki daya domin gudanar da wannan muhimmin aiki na al’umma.

“Ana bukatar a sake kiran Hon. Jaji ba za a iya wuce gona da iri ba, domin ya gaza wakiltar mazabarsa a daidai lokacin da ake bukatar ayyukansa.”

Hon. Aminu Sani Jaji

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here