Hukumar ci gaban Arewa maso Gabas (NEDC) reshen jihar Gombe, ta gina katanga daya na ajujuwa uku tare da bayar da wasu muhimman kayayyaki da suka hada da kujeru da kayan karatu da rubutu ga makarantar firamare ta Jauro Abare da ke karamar hukumar Gombe.
Hakan dai na daga cikin kokarin da hukumar ke yi na baiwa al’umma tallafi da kuma tallafawa harkokin ilimi don rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Haka zalika ta tabbatar da cewa ba wai iya yaran da basa zuwa makaranta ka dai wannan abu ya shafa a yankin ba, har ma da jihar baki daya.
Ko’odinetan hukumar, Rufa’i Lawan Baba, ya bayyana muhimmancin samarwa daliban kayan aiki da za su iya amfani da su, da kuma sa su samu nasara a harkokinsu na ilimi.
Ya kara da cewa hukumar na sane da cewa yawan daliban ya karu don haka akwai bukatar a samar da karin ajujuwa da sauran kayan da ake bukata domin baiwa makarantar da daliban damar samun karatu mai inganci, tare da yin kira ga iyaye da su tabbatar ana kai yaran makaranta akai-akai domin su samu cimma burinsu na rayuwa mai kyau.
Hajiya Yawoji Ahmad sakatariyar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Gombe (SUBEB) ta bayyana cewa, tallafin da hukumar ta bayar wani misali ne mai haske na irin karfin goyon bayan al’umma da hadin gwiwa wajen bunkasa ilimi da ingantawa.
Shima shugaban makarantar firamaren ta Jauro Abare, Malam Umar Sulaiman, ya nuna jindadinsa ga hukumar NEDC, bisa irin hazaka da jajircewar da suke yi na tallafawa harkokin ilimi a tsakanin al’umma, inda ya ce ba shakka tallafin zai yi tasiri mai kyau ga kwarewar daliban da kuma samun nasarar karatu.