Burina shine naga na hada kan yan Jaridun Afrika – Shugabar Kungiyar Yan Jaridun Afrika Masu Magana Da Yaren Hausa

IMG 20240521 WA0018

Shugaban Kungiyar cigaban yan jaridun Afrika masu Magana da yaren Hausa, Hajiya Maryam Lauwali sarkin Abzin ta sha alwashin kawo karshen cin zarafin yan jaridun Africa, da kuma kare musu martabar su a idon Duniya.

Shugabar ta bayyana hakan ne ranar Alhamis a wata hira da ta yi da Jaridar Solacebase Hausa, a Jihar kano dake Najeriya.

Maryam ta bayyana takai cin ta ganin yadda ake wulakan ta yan jaridu da kin daukar su da muhimmmanci, bayan sune ginshiki na kawo cigaba a duniya baki daya.

Ta kara da cewa kungiyar zatai gwagwarmaya da ta kwarorinta na kasheshin duniya domin kawo sauyi a nahiyar Afrika.

Ta kuma bayyana takaicin ta ganin yadda ake hada kai da yan jaridun Najeriya da kuma na ragowar kasashen dake makotaka da Nijar wajan zagin shugan kasar na mulikn soja, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin nuna kwarewa da kuma rashin adalci.

“Sunana Hajiya Maryam Lauwali Sarkin Abzin, ni yar jaridace, kuma nice shugaban kungiyar cigaban yan jaridun Afrika masu magana da yaren Hausa, kuma ni babbar edita ce a fitatciyar jaridan nan mai suna Tauraruwar Afrika Magazine, wacce ake buga ta a jamhuriyar Nijar, kuma ana buga wannan jarida ne da yarika guda uku, wadanda suka hada da Faransanci, Englishi da kuma harshen Hausa.”

“Maka sudun zuwana Najeiya shine wata kungiya na kafa wacce zata hada kan yan jaridun Afrika masu da amfani da harshen Hausa, wanda shalkwatar kungiyar na jamhuriyar Nijar, shine mukai tattaki muka kawo wa yan uwan mu yan jarida dake Najeriya ziyara, domin yi musu tayin wannan kungiya, domin a kawo sauyi a cikin aikin jarida a Afrika.”

“Sanan wannnan kungiya tana da membobi a kasashen Afrika, don daga nan Najeriaya zan zaga kasahsen afrika domin cigaba da ganawa day an jaridu, gabanin babban taro da kungiyar zata hada bayan babbar sallah.”

“Wannan kungiyar zata yaki mummunan aikin da turawan mulkin mallaka suke mana a Afrika, na amfani da yan jaridun kasahehn mu, ana hada mu rigima, suna sa mana gaba a tsakanin mu.”

“Wannan kungiya na da shuwagabannin ta, sannan kuma idon mun gama babban taro na wannan kungiyar zamu nada wakilai na kasashen afrika, wadanda zasu cigaba da wakiltar kungiya da kuma yada manufofin ta.”

“Wannan taro za ayi shine a bayan babban sallah, sanan muna sa ran halartar manyan baki daga kasashen afrika da zasu zo wannan taron.”

A karshe ta kuma ja hankalin yan jarida da su gujewa yada labaran karya, domin hakan ba abu ne mai bullewa ba.

“Ina kuma jan halinkalin masu zagin shugabannin mu na mulkin soja a Nijar, don bai kamata ta ba, zagin shuwagabanni ba abune mai kyau ba, mu yan Nijar bazamu lamunci zagin shuwaganin mu ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here