Majalisar Legas: Tsohon shugaban majalisar Obasa ya jagoranci zama da mambobi 4

Mudashir Obasa 750x430

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa ya jagoranci zaman majalisar tare da wasu mambobi hudu a zauren majalisar.

Ana gudanar da taron ne bayan da jami’an tsaro suka tilasta bude kofofin zauren majalisar.

Da misalin karfe 3:30 na yamma, majalisar ta zaman har zuwa karfe 3:30 inda sama da wasu mambobin majalisar 26 ne suka kewaye ta amma suka ki shiga zauren majalisar bisa ga dukkan alamu suna biyayya da goyon bayan kakakin majalisar, Mojisola Meranda.

Labari mai alaƙa: Legas: Obasabda wasu mutane dauke da makamai sun kutsa cikin ofishin shugaban majalisar

Tun da farko dai, kamar yadda rahotanni suka bayyana, Obasa ya bayyana komawar sa a matsayin shugaban majalisar, yana mai cewa duk da cewa tsige shi tsari ne na tsarin mulki da dimokuradiyya, amma dole ne a aiwatar da shi ta hanyar da aka gindaya.

An tsige Obasa a matsayin kakakin majalisar ne a ranar 13 ga watan Janairu lokacin da yake kasar waje, inda aka nada Mojisola Meranda a matsayin magajinsa.

Sai dai ya kalubalanci tsige shi, yana mai tabbatar da cewa har yanzu shi ne halartaccen shugaban majalisar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here