Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya mamaye harabar majalisar.
Rahotanni sun ce, Obasa na tare da wasu jami’an tsaro, ya shiga ofishin shugaban majalisar da misalin karfe 12 na ranar Alhamis.
Lamarin ya biyo bayan janyewar hadiman shugaban majalisar, Mojisola Meranda kan harkokin tsaro.
Karin labari: Rikicin Majalisar Legas: AIT, Channels TV sun nemi afuwar DSS
Babban Sakataren Yada Labarai na Meranda, Segun Ajiboye, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani takaitaccen sako a ranar Alhamis, inda ya zargi Obasa da tawagarsa da kutsawa cikin ofishin.
Wata majiya daga tawagar Obasa ita ma ta ce “Muna wurin yanzu.”
Ko da yake a halin yanzu majalisar na hutun dole, sai dai rahotanni sun nuna cewa ta karfin tsiya an an bude kofofin ofishin shugaban majalisar.
Cikakken bayani na tafe…….