Yanzu-yanzu: Gwamnonin Jam’iyyar PDP sun halarci taron Gwamnoni a Abuja

Taron, Jam'iyyar, PDP, gwamnoni, halarci, Abuja
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da Gwamnan Jihar Edo da Godwin Obaseki da Gwamnan Jihar Taraba da Agbu Kefas sun isa masaukin Gwamnan Jihar Oyo Asokoro...

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da Gwamnan Jihar Edo da Godwin Obaseki da Gwamnan Jihar Taraba da Agbu Kefas sun isa masaukin Gwamnan Jihar Oyo Asokoro a babban birnin tarayyar Abuja domin halartar taron Gwamnonin Jam’iyyar PDP.

A cewar majiyoyin wasu sun hada da gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang da mataimakin gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ossai da mataimakin gwamnan jihar Delta Monday John Onyeme.

Karanta wannan: Hukumar EFCC ta sake bankado karar Emefiele kan zargin hada-hada

Kungiyar Gwamnonin PDP karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ta shirya tattaunawa kan halin da al’umma ke ciki da ya danganci matsalolin tsaro da tattalin arziki da kuma zaben Gwamnan Jihar Edo da ke tafe, da zaben fidda gwani na jam’iyyar da za’a yi ranar 22 ga watan Fabrairu.

Hadi da taron majalisar zartaswa na kasa da sauran abubuwan da suka shafi jam’iyyar ta PDP.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here