Hukumar EFCC ta sake bankado karar Emefiele kan zargin hada-hada

Emefiele, EFCC, hukuma, bankado, zargi
Hukumar EFCC ta sake bunciko shari’ar da ake yi wa tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele da aka dakatar bisa tuhumar sa da zamba a wata babbar kotu da ke Abuja...

Hukumar EFCC ta sake bunciko shari’ar da ake yi wa tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele da aka dakatar bisa tuhumar sa da zamba a wata babbar kotu da ke Abuja.

Idan ba’a manta ba hukumar EFCC ta tuhumi Emefiele da wasu tuhume-tuhume guda 20 da suka hada da hada baki da cin gajiyar da bai dace ba, da kuma cin amana da dai sauransu, wadanda duk ya musanta a ranar Juma’a.

Kafin EFCC ta shigar da kararrakin da aka yi wa gyaran fuska na bukatar sake gurfanar da shi, a baya an tuhume shi da laifuffuka shida, inda aka fara gurfanar da shi a ranar 28 ga watan Nuwambar shekarar 2023.

Karanta wannan: Uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu ta isa Kano

A wasu tuhume-tuhume da EFCC ta bayyana ana zargin Emefiele ya kirkiro takarda da ya danganta ta da fadar shugaban kasa kan batun masu lura da zabe mai dauke da kwanan watan 26 ga watan janairun shekarar da ta gabata, tare da lamba SGF.43/L.01/201.

An ce ya aikata laifin da ya saba wa sashe na 1 (1) cikin baka na dokar damfara da sauran laifukan da suka shafi zamba, kuma hukuncin da aka yanke a karkashin sashe na 1 (3) cikin baka na wannan dokar.

A bisa gyaran da aka yi mata mai lamba CR/577/2023, Emefiele a ranar 8 ga Fabrairu na 2023, ya hada baki da Odoh Ocheme wanda a halin yanzu yake kokarin samun Dala Milliya 6.2 daga bankin CBN, ya ce SGF ne ya nemi gabatar da wata wasika mai kwanan wata 26 ga watan janairun 2023 tare da lamba SGF.43/L.01/201.”

Karanta wannan: ‘Yar Najeriyar da ke fatan zuwa Legas daga London a mota ta isa Afirka

EFCC ta kuma zargin cewa kwangilar gyaran masaukin Gwamnan CBN da ke Lamba 2 Glover Road da Ikoyi da Legas an bawa wani kamfani Architekon Nigeria Limited “inda biyun ke zama daraktoci da masu hannun jari masu rinjaye.”

A cewar EFCC ya saba wa tanadin sashe na 17 da 19 na cin hanci da rashawa da sauran laifukan da aka kayyade na cikin 2000.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here