‘Yar Najeriyar da ke fatan zuwa Legas daga London a mota ta isa Afirka

'Yar Najeriya, fata, zuwa, legal, london, afrika
Matar nan yar Najeriya, Pelumi Nubi ta isa Afirka a kokarin da take na zuwa Legas daga London a mota. Ta tsara bi ta kasashe 17 cikin nisan da bai wuce kilo...

Matar nan yar Najeriya, Pelumi Nubi ta isa Afirka a kokarin da take na zuwa Legas daga London a mota.

Ta tsara bi ta kasashe 17 cikin nisan da bai wuce kilomita dubu bakwai ba da burin isa Legas cikin wata biyu.

Matar mai shekara 29 tana wallafa bayanan yadda bulaguron na ta ke kasancewa daga Paris a Faransa bayan da ta bar Ingila a farkon watan nan.

Karanta wannan: Uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu ta isa Kano

A ranar Lahadi, ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram bayan da ta isa Moroko.

Hanyoyin da za ta bi sun hada da Yamma da hamadar Sahara da Mauritaniya da Senegal da Gambia da Guinea Bissu da Saliyo da Laberiya da Mali da Burkina Faso da Ivory Coast da Ghana da Togo da Benin sai Najeriya inda za ta yada zango a Legas.

Ms Nubi na ganin ita ce mace bakar fata ta farko da ke wannan yunkuri.

Ta jaddada cewa burinta ba shi ne kafa tarihi ba sai dai tana son nunawa duniya cewa za ta iya abin da ba’a yi zato ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here