Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bawa matar shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu sako zuwa mai gidanta wato shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sarkin ya nemi mai dakin Tinubu da ta isar da sakon da masarautar ta samu daga al’umma ga shugaba Tinubu cewa al’umma na fama da yunwa sakamakon tsadar kayan masarufi da ake fama da shi a wannan lokaci.
Karanta wannan: Super Eagles: Ahmed Musa da wasu sun yi kira a daina sukar dan wasa Iwobi
“Kayan abinci ya yi tsada. Mutane na shan wahala. Muna samun sakonni daga al’umma da muke shugabanta. Duk da cewa ba abu ne da ya fara yanzu ba. Amma tunda ku Allah ya dorawa shugabancin alhakin warware matsalar ya rataya a wuyanku,” in ji Sarkin Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi wannan magana ne a jiya Litinin a fadarsa yayin da matar shugaban kasar ta ziyarci fadar a birnin Kano.
Sarkin ya kara da cewa “sai kuma abu na biyu. Matsalar tsaro na addabar jama’a duk da cewa shi ma wannan ba lokacinku ya fara ba amma kasancewar su suke shugabanci to su ne Allah ya dorawa nauyin.”
Karanta wannan: “Najeriya Talaka Ce” – Martanin fadar Shugaban Kasa ga Sarkin Kano
Daga karshe mai martaba Sarkin na Kano ya nemi da gwamnatin tarayya ta waiwayi batun dauke wani sashe na babban bankin kasa da hukumar da ke sanya ido kan tashi da saukar jirage ta kasa daga Abuja zuwa birnin Legas.
“Muna kira ga shugaban kasa da a waiwayi wadannan batutuwa idan akwai kuskure sai a gyara” In ji Alhaji Aminu Ado Bayero.
Sarkin ya ce sakon zai fi saurin zuwa kunnuwan shugaban kasancewar uwargidansa aka bai wa sakon.