‘Yan bindiga sun kashe akalla mutum shida, ciki har da wata mata a ƙananan hukumomin Rafi da Wushishi na jihar Neja.
Rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutane sama da 50 tsakanin ranakun Talata da Laraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yi wa al’ummomin Yakila da Hana-wanka da kuma Kundu ƙawanya har zuwa wayewar garin Laraba.
Sai dai mazauna garuruwan sun ce daga baya dakarun sojin sama ta Najeriya sun kawo musu ɗauki, inda suka ɗauki sa’o’i da dama suna artabu da ‘yan bindigar kafin su fatattakesu.
Har ila yau, mazauna garin sun ce an kashe wasu ne lokacin da ake artabu tsakanin ‘yan bindigar da kuma sojoji.
Sun kuma ce an ɗauki gawarwakin waɗanda aka kashe zuwa Minna babban birnin jihar a safiyar ranar Laraba.
Jihar Neja dai na cikin jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da kuma ta masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, inda sanadiyyar hakan mutane da dama sun rasa rayukansu da kuma ɗaiɗaita da yawa.













































