Gwamnan Kano ya tabbatar da bunkasa tattalin arziki a jihar Kano

Abba Kabir Yusuf, Gwamnan, Kano, tabbatar, bunkasa, tattalin, arzki, jihar
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, a ranar Laraba ya yi alkawarin samar da yanayi mai kyau ga masu son zuba jari a yankin domin bunkasa tattalin arziki...

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, a ranar Laraba ya yi alkawarin samar da yanayi mai kyau ga masu son zuba jari a yankin domin bunkasa tattalin arziki.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa ta sada zumunta tsakanin Gwamna da Sakatariyar zartarwa ta Hukumar Bunkasa Zuba Jari ta Najeriya (NIPC), Hajiya Aisha Rimi, a gidan gwamnatin Kano.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya jaddada kudurin gwamnatin jihar na karfafa zuba jari da kuma bunkasa tattalin arziki.

Karin labari: Zargin Zamba: Tsohon Akanta-Janar na kasa ya nemi dage shari’a don mayar da kudin da ake zarginsa

Ya ce: “Mun kuduri aniyar samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari a jihar mu. Bisa la’akari da muhimmiyar rawar da saka hannun jari ke takawa wajen tsara yanayin tattalin arzikin Jihar Kano, a shirye muke mu ba da goyon bayan da ya dace don cimma wannan buri.

“Ta hanyar hadin gwiwa tare da gwamnatin tarayya, muna da burin samar da cikakkiyar damar jihar Kano a matsayin wurin zuba jari.

“Tare, za mu iya jawo hankalin masu zuba jari da za su ba da gudummawa sosai ga ci gaban tattalin arzikin jiharmu.”

Sakatariyar zartaswar hukumar bunkasa zuba jari ta Najeriya, Hajiya Aisha Rimi, ta bayyana jihar Kano a matsayin babbar cibiyar zuba jari a Arewacin Najeriya, inda ta jaddada bukatar jawo masu zuba jari zuwa yankin.

Karin labari: Tinubu Ya Ƙirƙiro Ma’aikatar Harkokin Kiwon Dabbobi

Ta tabbatar da aniyar NIPC na inganta tattalin arzikin Kano ta hanyar tallafawa masu zuba jari na cikin gida da kuma saukaka ci gaban su.

Ta ce: “Muna da himma wajen shigar da ƙungiyoyin jin kai tare da haɓaka cikakkiyar fayil ga masu saka hannun jari.

“Wannan shiri zai saukaka hanyoyin da masu zuba jari na kasashen waje za su binciko tare da samun damammaki a cikin Kano.”

Ta kuma yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa gagarumin nasarorin da ya samu a fannin ilimi, kiwon lafiya da tsaro, inda ta bayyana cewa wadannan ci gaban da aka samu sun samar da kwanciyar hankali da walwala ga masu zuba jari na gida da waje.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here