Kungiyar kwadago NLC ta bayyana cewar idan har tsadar rayuwar da kasar ke fama da shi ya ci gaba ko shakka babu basu da zabin da ya wuce su mika bukatar neman Naira Miliyan 1 a matsayin mafi karancin albashi.
A wata zantawarsa da manema labarai Joe Ajaero ya koka da yadda rayuwa ke ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya tsada tun bayan hawa mulkin shugaba Bola Tinubu sakamakon cire tallafin man fetur da wasu manufofin kudi da ya ce dole su kalubalance su.
Karanta wannan: Ministan tsaron kasar Laberiya ya yi murabus
Kafin yanzu dai NLC na neman Naira Dubu 200 ne a matsayin mafi karancin albashi kuma har zuwa wannan lokaci gwamnatin Najeriyar ba ta sahale bukatar ta su ba, sai dai Mista Joe Ajaero ya ce a wancan lokaci ana canza duk dalar Amurka guda ne akan Naira 800 zuwa 900 sabanin yanzu da farashin ke tasamma dubu 1 da 500.
Har zuwa yanzu dai ana biyan ma’aikatan Najeriyar ne naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi, kuma duk da haka wasu jihohin basu iya cika wannan matakin ba.
Karanta wannan: “Mun biya albashin ma’aikata na Janairu” – Gwamnatin Tarayya
Wasu rahotanni na cewa har zuwa yanzu akwai jihohin da ke biyan karancin albashi a kasa da dubu 10.
Tsadar rayuwa dai na ci gaba da tsananta a sassan Najeriya bayan da farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi inda ake sayar da buhun shinkafa a farashin Naira Dubu 60 zuwa 70.
A bangare guda ana sayar da duk buhun masara guda daya a farashin Naira Dubu 56.