Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce jami’anta uku na kwance a asibiti sakamakon harbin bindiga da aka yi musu a Abuja.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce an kai wa jami’an hari ne a unguwar Jahi da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin wani samame da aka kai kan wani gini da ba a kammala ba a yankin NNPC da ke Jahi, biyo bayan bayanan sirri da kuma sa ido.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da kwalaben codeine 74, lita 10 na syrup codeine, gram 48 na tramadol 225mg, kilogiram 4.9 na skunk, da wayoyin Android guda biyar.
A cewarsa, yayin da tawagar ta fito daga wurin ne aka yi ta harbe-harbe.
“Jami’an uku sun samu raunuka harbin bindiga – daya a hakarkarinsa, wasu biyu kuma a baya da kafa.
Karin karatu: Easter: An kashe mutane 17 a hare-haren da aka kai wa al’ummar Benue – ‘Yan sanda
“An fara kwantar da su ne a asibitin ‘yan sanda da ke Unguwar Garki 1, kafin a kai su Asibitin kasa da ke Abuja, don ci gaba da kula da su,” inji shi.
Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya janar Buba Marwa mai ritaya ya bayyana godiya ga ma’aikatan asibitin ‘yan sanda bisa gaggawa da suka yi.
Marwa ta kuma godewa babban daraktan kula da lafiya na asibitin kasa bisa yadda da kan sa yake kula da jinyar jami’an bayan an tuntube su.
Yayin da yake bakin aiki a Kano, Marwa ya tattauna da jami’an da suka jikkata ta wayar tarho inda ya yi musu fatan samun lafiya cikin gaggawa.
Ya kuma ba su tabbacin cewa hukumar za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro domin zakulo wadanda suka kai harin. (NAN)













































