Easter: An kashe mutane 17 a hare-haren da aka kai wa al’ummar Benue – ‘Yan sanda

Gunmen 2

Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta ce wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari tare da kashe mutane 17 tare da raunata da dama a kananan hukumomin Logo da Ukum na jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Juma’a, mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Sewuese Anene a Makurdi.

A cikin sanarwar, Anene, ya bayyana cewa an kashe mutane biyar a Ukum sai 12 a karamar hukumar Logo, ya kara da cewa wasu sun samu raunuka kuma suna karbar magani.

“An ceto mutane biyar a yankin Gbagir kuma an kai su asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsu.

“Abin takaici, an kai wani harin da ba a yi tsammani ba a lokaci guda a Logo, inda aka kashe mutane 12 kafin zuwan ‘yan sanda, wanda ya kai adadin mutane 17.

Anene ya gargadi masu amfani da shafukan sada zumunta wadanda ke bayar da rahotannin da ba a tabbatar da su ba tare da tunzura jama’a da su guji irin wannan aika-aika.

Kakakin ‘yan sandan ya ce irin wadannan ayyuka na iya haifar da tashin hankali da bai kamata ba a jihar. (NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here