Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce dangantakarsa da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tana nan daram, babu wata matsala tsakaninsu.
Yusuf ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Mustapha Muhammad, ya fitar a Kano ranar Laraba.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin wani taron tunawa da zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso karo na 69 da aka gudanar a ƙaramar hukumar Madobi, a matsayin wani ɓangare na bukukuwan murnar zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan.
Ya kuma sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin manufofin tafiyar Kwankwasiyya da suka shafi ci gaban jihar Kano da inganta rayuwar jama’a.
Gwamna Yusuf ya ce duk wanda yake sa ran samun rabuwar kai a cikin tafiyar Kwankwasiyya zai gamu da babban takaici, yana mai yabawa tarihin jagorancin Kwankwaso tun daga ƙuruciyarsa har zuwa lokacin da ya zama shugaba.
Haka kuma, gwamnan ya gode wa Farfesa Kamilu Fagge da Farfesa Bello Kano bisa addu’ar da suke yi domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.
A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya nuna farin ciki da irin cigaban da gwamnatin Yusuf ke samu, tare da godiya ga jama’ar Kano da wajen jihar da suka halarci bikin zagayowar ranar haihuwarsa.











































