Tsohon Ministan Jonathan ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP

pdp 1 750x430 (1)

Tsohon Ministan Ayyuka na Musamman a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Kabiru Tanimu Turaki, ya zama ɗan takarar da aka amince da shi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa a babban taron jam’iyyar da za a gudanar a watan gobe.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ne ya sanar da wannan mataki bayan taron shugabannin PDP na arewa da aka gudanar da daren Laraba a Abuja.

Fintiri ya ce an cimma matsayar ne bayan shawarwari masu faɗi tsakanin shugabannin yankin arewa na jam’iyyar, inda suka amince da Turaki a matsayin ɗan takarar da za su goyi baya.

Sai dai ya bayyana cewa wannan matsayar ba ta hana sauran ‘yan jam’iyyar da ke da niyyar takara shiga zaɓe ba, domin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na bai wa kowane memba ‘yancin neman mukami a babban taron jam’iyyar.

Daga cikin manyan jiga-jigan da suka halarci taron akwai shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum; gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; gwamnan Bauchi, Bala Muhammad; tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau; da tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi, da sauransu.

Rahotanni sun nuna cewa PDP ta bar kujerar shugabancin jam’iyyar a yankin arewa, inda daga bisani aka ƙayyade ta ga yankin Arewa maso Yamma, wanda Turaki daga jihar Kebbi ya fito.

Haka kuma, taron shugabannin yankin arewa ya yanke shawara kan wasu muƙamai da aka ware wa yankin kamar Sakatare na Ƙasa, Ma’aji da Shugaban Matasa na Ƙasa, da sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here