Babu inda zai je: NNPP ta musanta rade-radin sauya shekar Kwankwaso

FB IMG 1697844439662 1 720x430 (1)

Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) reshen jihar Kano ta musanta rade-radin da ake yadawa cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar a jihar Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a a Kano.

Dungurawa ya ce Kwankwaso ba ya bukatar tuntubar kowa kafin ya yanke shawarar siyasa, amma ya jaddada cewa babu wani shiri na sauya sheka.

Karanta: APC ta yi da martani kan jita-jitar sauya shekar Kwankwaso

“Ba mu da wata alaka da APC, kuma ba mu da niyyar sauya sheka,” in ji Dungurawa, inda ya yi watsi da jita-jitar a matsayin barna.

Ya kuma bayyana kwarin guiwar cewa gwamnatin NNPP a jihar Kano na daukar matakai tare da dawo da doka da oda a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa manema labarai sun ruwaito shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano yana cewa kofar jam’iyyar a bude take ga Kwankwaso da sauran ‘yan Najeriya da ke son sauya sheka. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here