Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta ce ta fara gudanar da bincike kan harin da aka kai gidansu Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jam’iyyar PDP mai wakiltar Kogi ta tsakiya a Obeiba-Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Ovye-Aya, ya sanyawa hannu a ranar Juma’a a Lokoja ta ce binciken ya biyo bayan rahoton da aka samu cewa wasu ‘yan daba ne da ba a san ko su wanene ba suka kai wa gidan hari.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Miller Dantawaye, ya umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashen binciken manyan laifuka da ya fara gudanar da bincike cikin gaggawa kan harin da aka kai, domin tabbatar da kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su gaban kotu.
Ya kara da cewa, a wannan ranar da misalin karfe 01: 00 na safe wasu ‘yan bindiga kimanin su uku dauke da muggan makamai suka kai farmaki gidan gidansu Sanatan inda suka lalata wasu gilashin gaban taga.
Labari mai alaƙa: Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidansu Sanata Natasha Akpoti a Kogi
Ya bayyana cewa bisa la’akari da rahoton da ake zargi, CP ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa don tabbatar da sahihancinsa tare da magance lamarin kamar yadda aka zata.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sanata Akpoti-Uduaghan, wadda ta yi magana a kan lamarin, ta ce ‘yan bindigar da ake zargin sun dauka tana cikin garin ne don haka suka kai hari gidan ‘yan uwanta a ranar Talata da daddare.
Ta ce a yayin harin jami’an tsaro da jama’ar gari sun mayar da martani tare da fatattakar su. (NAN)