Mai neman takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Abdussalam Abdulkarim Zaura, ya rasa mahaifinsa, Alhaji Abdulkarim Saleh Zaura, wanda ya rasu yana da shekaru 108 bayan doguwar jinya.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa dattijon ya rasu ne a safiyar Lahadi.
Alhaji Abdulkarim ya rasu ya bar ‘ya’ya shida, jikoki, da sauran ‘yan uwa.












































