Shugaba Bola Tinubu ya sauya ranar fara tafiyarsa kasashen uku zuwa ranar Lahadi, maimakon Asabar kamar yadda aka sanar a baya.
Bayyana samun sauyi na cikin wata Sanarwar da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ta shafinsa na X ranar Asabar.
Onanuga ya rubuta, “Shugaba Tinubu ya sauya tafiyarsa ta kasashen uku zuwa ranar Lahadi, maimakon Asabar kamar yadda aa bayyana baya.”
Babu wani cikakken bayani kan dalili nan take game da sauya jadawalin.
Idan za a iya tunawa cewa an shirya Tinubu zai bar Abuja ranar Asabar don ziyarar aiki a kasashen Faransa, Kenya da Ruwanda.
A cewar wata sanarwa da Onanuga ya fitar ranar Juma’a, tafiyar za ta fara da Faransa kafin a wuce Nairobi, Kenya.
Ana sa ran Tinubu zai halarci Taron Afrika da Faransa a Nairobi, wanda Emmanuel Macron da William Ruto za su jagoranta tare.
Taron, wanda aka shirya yi daga 11 zuwa 12 ga Mayu, zai mayar da hankali kan batutuwa da suka haɗa da sauya makamashi, sauyin fasahar zamani da ɗaukar mataki kan sauyin yanayi.











































