Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Ta’annati EFCC ta kama wasu mutum 14 da ake zargi aikata zamba ta intanet
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama mutanen ne ranar Juma’a, 5 ga watan Mayun a Fatakwal babban birnin jihar Rivers.
Hukumar ta kuma wallafa sunayen mutanen da ta ce ta kama a lokacin wani samame da ta kai a yankin Rumuekini.
An kama su da motoci uku, ta kwafutoci da wayoyin hannu da wasu na’urorin daban-daban.
EFCC ta ce za ta gabatar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.