Na so ƴa ƴa na su yi fim amma sai suka ƙi yarda – Ali Nuhu

1683459369567
1683459369567

Shahararren jarumi, mai shirya finafinai kuma mai bada umurni a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana cewa ya so ƴaƴan sa su yi harkar fim amma sai suka zaɓi bin wata hanyar daban.

Ali Nuhu ya bayyana cewa, ɗan sa Ahmad mai shekara 16 a duniya, ya nuna yana son harkar ƙwallon ƙafa, yayin ɗiyarsa Fatima, ta ke son karantar dangatakar ƙasa da ƙasa a jami’a.

Jarumin a wata hira da BBC Hausa, ya yi watsi da kalaman da ake jifar ƴan fim da su kan cewa, ba su son yin fim tare da ƴaƴan su. A kalamansa:

“Maganar gaskiya na fi son ɗa na ya zama jarumi, amma ya nace cewa yana son zama ɗan ƙwallo. Don haka sai na goya masa baya, saboda a zamanin yanzu ba a takurawa ƴaƴa kan abinda kake so su zama.”

“A matsayin mahaifi idan ka gano abinda ƴaƴan ka su ke son zama, sai ka goya mu su baya. Ni a ƙashin kai na fi son mu yi fim tare amma sai ya nuna ɗan ƙwallo ya ke son zama.”

“Fatima ta nuna ba ta son fim lokacin tana da shekara 13 a duniya. Tana son karantar dangantaƙar ƙasa da ƙasa a jami’a, a yanzu haka ta kusa kammala 300L. Kuma Alhamdulillahi da goyon bayan da mu ke bata tana ɗaya daga cikin ɗalibai masu CGP babba a ajin su.”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here