Shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya yi watsi da ficewar wasu ‘yan majalisar tarayya daga jam’iyyar a baya-bayan nan, yana mai bayyana su a matsayin ba su da wani kataɓus a siyasance gabanin babban zabe na shekarar 2027.
Dungurawa ya bayyana sunayen Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum da Ali Sani Madakin Gini, inda ya bayyana cewa babu daya daga cikinsu da ke da karfin siyasar yin barazana ga damar jam’iyyar NNPP a zaben mai zuwa.
A wata hira ta musamman da ya yi da gidan Talabijin na SolaceBase, Dungurawa ya ce tuni jam’iyyar ta dakatar da ‘yan ukun tun kafin ficewarsu saboda abin da ya bayyana a matsayin “rashin alkiblar siyasa.
“An san su da rashin mutunta dattawan jam’iyya wanda ya sa aka dakatar da su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, ficewarsu ba asara be ce ga jam’iyyar, ya na mai cewa jam’iyyar NNPP ba ta taɓa jin daɗin yadda suke gudanar da ayyukansu ba.













































