Wata babbar kotu da ke Abuja ta soke umarnin kama Kabiru Tanimu Turaki, wanda ake zargi a matsayin shugaban wani bangare na PDP, bayan ya bayyana a gaban kotu da kansa.
Alkalin kotun, Justice Peter Kekemeke, ya yanke wannan hukunci ne bayan lauyan Turaki, Chris Uche SAN, ya gabatar da bukatar baki tare da neman afuwar rashin halartar zaman da ya gabata.
Lauyan ya bayyana cewa yana wajen ƙasar a lokacin da aka yi zaman kotun na baya, amma ya dawo cikin ƙasar a ranar Laraba kuma ya nufi kotu kai tsaye.
Haka kuma ya nemi afuwa a madadin wanda yake karewa, yana mai cewa rashin halartar kotun ba da gangan ba ne.
Ya kuma nuna cewa domin nuna gaskiya, zai janye bukatar da suka shigar na dakatar da aiwatar da umarnin kama Turaki, tare da bayyana cewa a shirye yake ya amsa tuhumar da ake masa.
A nasa bangaren, lauyan masu ƙara, Usman Rabiu, ya bayyana cewa ba su da wata adawa da bukatun da lauyan Turaki ya gabatar, yana mai cewa manufar bayar da umarnin kama shi ita ce a tilasta masa bayyana a kotu.
Alkalin ya lura cewa Turaki ya halarci kotu da kansa kafin a aiwatar da umarnin kama shi, tare da cewa lauyansa ya nemi afuwa kan rashin halarta, duk da cewa bai fayyace dalilin ba.
Saboda haka, kotun ta amince da bukatar, ta kuma soke umarnin kama shi, sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 22 ga Afrilu domin ci gaba da sauraron tuhume-tuhumen da ake masa, wanda ya haɗa da zargin bayar da bayanan ƙarya ga ‘yan sanda.













































