Wata kotun majistare a Kano ta bayar da beli ga Suleiman Yakubu, direban da ke aiki ga matar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan zargin satar kayan ado.
An gurfanar da Yakubu tare da wasu mutane biyu, Idris Uba-Musa da Abdullahi Hassan, bisa tuhume-tuhumen hada baki, sata da karɓar kayan sata.
Sai dai kotu ba ta bayyana cikakken bayanin shekarunsu ko wuraren zamansu ba.
Mai gabatar da kara, Abubakar Ibrahim, ya bayyana cewa Yakubu wanda ke aiki a wajen matar sarkin, Sadiya Ado-Bayero, ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Maris a Kano.
Rahotanni sun ce wanda ake tuhuma ya shiga dakin matar sarkin ba bisa ka’ida ba inda ya sace kayan ado, da kudi Naira dubu dari biyar da kuma wayar Samsung smartphone, dukkaninsu da darajarsu ta kai Naira Miliyan 60.
A yayin shari’ar, Yakubu ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, yayin da sauran mutanen biyu suka musanta zargin da ake musu.
Lauyan wadanda ake tuhuma ya roki kotu ta bayar da beli, inda mai shari’a Hadiza Abdurahman ta amince da bayar da belin naira miliyan 10 ga kowannensu tare da sharadin kawo mutane biyu masu tsaya musu.
Kotun ta kuma shar’anta cewa dole daya daga cikin wadanda za su tsaya musu ya kasance uba ko dan uwa, yayin da dayan kuma dole ya kasance ma’aikacin gwamnati mai mataki na 15 ko sama da haka, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Afrilu.













































