Gwamnatin tarayya ta amince da karin kashi 25 cikin 100 na albashin ma’aikatan gwamnati da kashi 35 cikin 100 a kan sauran tsare-tsare guda 6 da suka shafi albashin ma’aikata.
Shugaban yada labarai na hukumar (NSIWC), Mista Emmanuel Njoku, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja.
Karin labari: Kamfanin NNPCL ya bayyana ranar da zai fara aikin matatar mai na Kaduna
“Gwamnatin tarayya ta amince da karin albashin ma’aikata tsakanin kashi 25 zuwa kashi 35 cikin 100 a kan sauran tsare-tsare guda shida na tsarin albashi.
“Ƙarin zai fara aiki daga 1 ga Janairu,” in ji shi.
A cewar Njoku, gwamnatin tarayya ta kuma amince da karin kudin fansho tsakanin kashi 20 zuwa kashi 28 cikin 100 na ‘yan fansho kan tsarin fayyace fa’ida.
Karin labari: “Jami’ar Maryam Abacha ta jawo tsadar filaye a yankin Hotoro a Kano” – Wakilan Filaye
Ya ce hakan ya kasance dangane da tsarin albashi guda shida da aka ambata a baya kuma zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu.
Ya ce matakin ya yi daidai da tanadin sashe na 173 (3) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).