Wani dalibin kwalejin koyon aikin gona ta Audu Bako da ke Dambatta a jihar Kano ya rasa ransa a wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya afku a safiyar ranar Talata, a babbar madatsar ruwa ta Thomas Dambatta.
Shugaban kungiyar daliban kwalejin Kwamared Jabir Karaye ne ya shaidawa SolaceBase cewa lamarin ya shafi dalibai guda biyu, kuma da yammacin ranar an tsinci gawar daya daga cikinsu.
Karin labari: Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashi ga ma’aikatan Gwamnati
Ya kara da cewa an dakatar da aikin ne a wannan rana kuma za a ci gaba da gudanar da bincike a safiyar Laraba da fatan gano dalibi na biyu da ya bata.
Al’ummar kwalejin na cikin kaduwa da alhini, inda dalibai da ma’aikata suka yi ta’aziyya da jaje ga iyalan daliban da abin ya shafa.
Sai dai ba a bayyana sunayen daliban da abin ya shafa ba.