Kungiyoyin NLC da TUC sunyi Allah-wadai da yunkurin karin kudin wutar lantarki

NERC, NLC, TUC, karin wuta, lantarki
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, sun yi kira ga Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) da masu aikin samar da wutar lantarki, da su sauya karin...

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, sun yi kira ga Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) da masu aikin samar da wutar lantarki, da su sauya karin kudin wutar lantarki cikin mako guda.

Shugaban kungiyar, Mista Joe Ajaero da Mista Fetus Osifo ne suka yi wannan kiran a ranar Laraba a wani jawabi na hadin gwiwa don bikin ranar ma’aikata ta 2024 a Abuja.

Kungiyoyin biyu sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake fama da matsalar wuta a kasar da ke shafar ci gaban tattalin arzikin kasar.

Karin labari: Wani dalibi ya mutu tare da bacewar wani a jirgin ruwa a Kano

A cewarsu, ya zama wajibi duk wata al’ummar da ba ta iya sarrafa albarkatun makamashi yadda ya kamata, ta fuskanci wani lalacewa.

“Daya daga cikin muhimman abubuwan da ke dagula al’ummarmu shi ne gazawarmu a fili wajen gudanar da wannan fanni domin jin dadin rayuwar ‘yan kasa baki daya.

Sun ce yana da matukar muhimmanci ga gwamnati ta hada kai da jama’a don samar da tsare-tsare da ke tabbatar da samar da makamashi ga daukacin ‘yan Najeriya.

Karin labari: Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashi ga ma’aikatan Gwamnati

A cewarsu, yanayin da bangaren wutar lantarkin ke fuskanta ba ya canzawa cikin shekaru goma bayan mayar da bangaren zuwa kamfanoni.

“Dalilan sun bayyana a fili. Matukar dai wadanda suka siyar da kamfanonin sun kasance masu saye, ‘yan Najeriya za su ci gaba da fuskantar manyan kalubale a fannin wutar lantarki.

”Rashin da’a ne a tilasta wa ‘yan Najeriya biyan kudin wutar lantarki da babu shi”  in ji kungiyoyin biyu, kamar yadda NAN ta rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here