Kotu ta dage sauraron bukatar neman beli na El-Rufai

Nasir El Rufai Kaduna (2)

Wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta dage sauraron bukatar beli da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya gabatar zuwa ranar 14 ga watan Afrilu.

Mai shari’a Rilwanu Aikawa ne ya sanya sabon ranar bayan sauraron hujjoji daga bangaren kariya da na masu gabatar da kara a ranar Laraba.

An gurfanar da El-Rufai ne daga hukumar (ICPC) kan tuhume-tuhume guda 10 da suka hada da karkatar da dukiyar gwamnati da kuma wanke kudade.

Sai dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa a gaban kotu.

Kotun ta umarci a ci gaba da tsare shi a hannun ICPC har zuwa ranar da za a saurari bukatar belinsa.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan ya isa harabar kotun da misalin karfe 9 na safe cikin wata mota kirar Toyota Hilux baki, tare da rakiyar jami’an Department of State Services (DSS).

Bayan kammala shari’ar, daya daga cikin lauyoyinsa, Ubong Akpan SAN, ya tabbatar da dage zaman kotun, yana mai cewa shugaban tawagar lauyoyin zai yi karin bayani daga baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here