Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi mambobin wata kungiyar masu satar adaidaita sahu ne, tare da kwato adaidaita sahu guda takwas da aka sace a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan wani samame da jami’an ‘yan sanda na ofishin Kwakwachi suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.
Rahoton ya nuna cewa nasarar ta samu ne a ranar 26 ga Maris, 2026 da misalin karfe 5 na yamma, lokacin da jami’an ‘yan sanda ke sintiri a kan titin filin jirgin sama a Kano, inda suka kama wani da ake zargi mai suna Abubakar Sidi daga kauyen Kunkumi na jihar Kaduna, yana tukin adaidaita sahu mai lamba NSR 85 WD da kuma lambar Karota KMC 1084.
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya kasa bayar da gamsasshen bayani kan mallakar adaidaita sahun, lamarin da ya sa aka mika shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda.
Daga bisani, jami’an bincike sun gano cewa wanda ake zargin ya yaudari mai adaidaita sahu a kan titin gidan sarki na Kano, kafin ya hada baki da sauran mambobin kungiyar wajen satar motar.
Binciken ya kara kai ga cafke wasu karin mutane biyu, wato Abba Babura da Babangida Haruna, yayin da aka kuma gano wasu karin adaidaita sahu guda bakwai da aka sace, wadanda aka sayar da su a garin Babura da ke jihar Jigawa.
Rundunar ‘yan sanda ta shawarci masu sana’ar adaidaita sahu da su kara yin taka-tsantsan wajen mu’amala da fasinjoji, tare da gargadin su da kada su karbi abin sha ko kyauta daga bakin mutane da ba su sani ba, sannan ta bukaci al’umma da su rika kai rahoton duk wani abin da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro.













































