Gwamnati za ta samar da gidauniyar taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, sauran masifu – Tinubu

Tinubu Flood 750x430

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin tarayya za ta samar da gidauniyar bayar da tallafi ga ‘yan Najeriya wadanda ambaliyar ruwa da sauran bala’o’i suka shafa.

Shugaban ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai jihar Borno, inda ya jajanta wa gwamnati da mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a yankuna daban-daban sakamakon ambaliya da madatsar ruwa ta Alau.

Ya kuma jaddada muhimmancin asusun, inda ya ba da misali da rashin hasashen sauyin yanayi da kuma kara lallacewar yankuna da dama a fadin kasar.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta hada kai da kamfanoni masu zaman kansu domin kafa asusun tallafawa.

Ya samu rakiyar shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, wanda ya bayyana aniyar majalisar ta yi aiki da bangaren zartarwa wajen kafa asusun.

A yayin ziyarar tasa, Tinubu ya kuma tsaya fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn El-Kanem, sansanin ‘yan gudun hijira a makarantar sakandiren gwamnati da ke Maiduguri, inda ya zagaya wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa.

“Bayan na ziyarci Shehun Borno da sansanin ‘yan gudun hijira, na yi ta tunani kan yadda za a magance bala’o’i irin wannan da kuma illar sauyin yanayi,” in ji Tinubu.

“Dole ne a samar da asusun ba da agajin domin dalkile bala’o’i. Ina shirin shigar da kamfanoni masu zaman kansu don taimakawa wajen sake gina yankunan da abin ya shafa. Idan muka ware kaso kadan na FAAC ga asusun ba da agajin bala’o’i, hakan zai karfafa mana hadin kai da daukar nauyi.”

Tinubu ya bayyana jin dadinsa ga gwamnonin da suka bayar da tallafi ga jihar Borno da suka hada da gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq, gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu, da gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here