Kudade ne babban kalubalen gina tituna – Fashola

E6762368 6EC3 4775 8EA1 F986EE7A7E01
E6762368 6EC3 4775 8EA1 F986EE7A7E01

Ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Fashola (SAN), ya ce babban kalubalen da ke tattare da gina tituna a Najeriya shi ne na samar da kudade.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kayyade ayyukan tituna na gwamnatin tarayya a taron tattaunawa na matasan jam’iyyar APC a ranar Alhamis a Kano.

A cewar ministan, aikin gina tituna a Najeriya babban aiki ne wanda yake bukatar bata lokaci tare da samar da manyan kayan aiki.

Sauran kalubalen da ministan ya kuma gano su ne; hakkin hanya, diyya, yanayin yau da kullum,  yanayin kasa, rashin tsaro da hadarin gudanar da aikin, waɗanda duk ke haifar da tsaiko yayin aikin titin.

Fashola ya ce gwamnatin Buhari ta zo ne da samar da ababen more rayuwa a matsayin manufa kuma ta sanya jari mai yawa a wannan fanni cikin shekaru shida da suka gabata.

Ya zayyana wasu daga cikin manyan titunan da aka kammala kuma aka fara amfani da su a baya-bayan nan da suka hada da: titin Kebbi-Sokoto, Kontagora-Jega Koko, Kano-Jigawa-Azare da kuma titin Potiskum.

Har ila yau, a aikin gine-ginen gadoji, ministan ya ambaci gadar Nfon da ke jihar Cross Rivers wadda ita ce babbar hanyar sadarwa ta kasa da kasa da kasar Kamaru.

Ministan ya ci gaba da cewa, aikin titin Bonny-bodo wanda ke da manyan gadoji hudu da kananan guda takwas, tuni aka fara kammala aikin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wani bangare na ziyarar da ministar ta kai jihar Kano, ita ce duba ayyukan gidaje da hanyoyin gwamnatin tarayya na Kano da kewaye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here