Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta sanar da ayyana tsohon ministan harkokin man fetur na tarayya, Timipre Sylva, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin hada baki da karkatar da Dala Miliyan 14,859,257.
Sanarwar ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Bayelsa yana cikin wadannan ake bincike kan kudaden da hukumar raya harkokin man fetur ta Najeriya (NCDMB) ta zuba a kamfanin Atlantic International Refinery and Petrochemical Limited domin gina matatar mai.
Sanarwar ta ce wannan mataki ya biyo bayan umarnin kama shi da babbar kotun jihar Legas ta bayar a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2025.
Hukumar ta nemi duk wanda ke da wani muhimmiya bayani game da inda Sylva yake da ya tuntubi ofisoshinta da ke Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Port Harcourt ko Abuja, ko kuma ta wayar 08093322644 ko imel info@efcc.gov.ng ko a kusa da ofishin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Sanarwar ta kuma tunatar da cewa Timipre Sylva, wanda ke da shekaru 61, ɗan asalin ƙaramar hukumar Brass ne a jihar Bayelsa.













































