An yi jana’izar dan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar karamar hukumar Giwa Rilwan Aminu Gadagau wanda ‘yan bindiga suka hallaka a yayin wani hari da suka kai ranar litinin a hanyar Kaduna zuwa Zaria.
An gudanar da sallar jana’izar ne a Masallacin juma’a na Haruna Danja dake Tudun Wada a Zaria.
Sallar jana’izar ta samu halartar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai da kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Ibrahim Zailani da sauran masu ruwa da tsaki a jihar ta Kaduna.
Wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin ciki na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar ta ce, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nuna kaduwar sa dangane da kisan gilla da aka yi wa dan majalisar.
Gwamnan ya yi adduar Allah ya gafarta masa tare da sauran mutanen da suka rasa rayukan su a yayi harin, da sauran hare-haren ‘Yan bindiga.













































