Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya halarci sallar jana’izar ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna, Rilwan Aminu Gadagau da aka kashe.
‘Yan bindiga sun harbe Rilwan Aminu Gadagau wanda ke wakiltar mazabar Giwa ta yamma ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Litinin
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ta ce kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani da kuma masallatan Juma’a na Haruna Danja da ke Tudun Wada a garin Zaria sun tarbi gwamnan.
Yace ‘’ Gwamnan bayan sallar jana’izar ya bayyana Gadagau a matsayin dan majalisa mai jajircewa da sadaukarwa ga al’ummar mazabarsa da ma jihar baki daya.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan sa, da kuma rayukan sauran ‘yan kasar da suka rasa rayukansu a hare-haren baya-bayan nan da aka kai a jihar,” in ji sanarwar.













































