Hukumomi a arewacin Indiya sun ce mata da ‘yan mata 13 ne suka mutu a lokacin da suka fada rijiya a yayin wani bikin aure.
Lamarin ya faru ne a daren Laraba a kauyen Nebua Narangia da ke gundumar Kushinagar ta jihar Uttar Pradesh.
Wadanda abin ya shafa dai na tsaye ne a jikin wani karfe wanda aka lullube rijiya da shi a tsakar gida a lokacin da suke kallon yadda ake gudanar da bikin haldi, wanda daya ne daga cikin al’adu da dama da ke cikin bikin auren Hindu, kuma a lokacin ana shafa wa ango turmeric.
Karfen ya ruguje saboda nauyinsu kuma sama da mutane 20 ne suka fada cikin rijiyar, kamar yadda alkalin gundumar Kushinagar S. Rajalingam ya bayyana.
Mutane 11 ne suka mutu a nan take sannan an ceto 15, amma biyu daga cikinsu sun mutu a asibiti.
Firayim Minista Narendra Modi ya ce mutuwar ta yi matukar tayar da hankali kuma hukumar gundumar tana yin duk mai yiwuwa don taimakawa wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda suka mutu.













































