A yammacin yau laraba Allah ya karbi rayuwa shahararren dan wasan fim din Hausa Sani Garba SK, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke unguwar Nasarawa a cikin birnin Kano.
A baya dai an sha yada jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa da kansa.
Wani Furodusa a masana’antar Kannywood Abdul Amart ya tabbatarwa da BBC rasuwar Sani SK, inda ya bayyana cewa tuni aka tafi da gawar mamacin gida, kuma za a yi jana’izarsa a gobe Alhamis da safe.