A yau Alhamis ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya domin halartar taron haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka karo na uku wanda shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya zai karɓi baƙunci.
Mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau a birnin tarayya Abuja.
A cewar masu shirya taron, taken sa shi ne ” Samar da ingantacciyar hadin gwiwa don samun ci gaba da ƙaruwar arziki” yayin da kuma yake da maudu’in yin nazari kan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da Turkiyya tun bayan taron ƙarshe na shekarar 2014 da aka gudanar.
“Taron hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka na ukun dai yana zuwa ne a daidai bayan da shugaba Erdogan ya kawo ziyarar aiki Najeriya a kwanakin baya, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama a fannonin makamashi harkokin tsaro sai haƙar ma’adinai da ma’adinan ruwa duk domin ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
“Shugaban na Turkiyya a ziyarar da ya kawo Najeriya, ya tabbatar da aniyarsa ta gaggauta faɗaɗa harkokin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu zuwa dala biliyan biyar, kuma tawagar Najeriya za ta yi amfani da damar taron da za a yi a Istanbul domin inganta haɗin gwiwa da sauran abokan hulɗar kasuwanci, ƙarin damar kasuwanci da zuba jari a kasar.
Sanarwar ta ce “Ana sa ran taron zai samar da ƙa’idoji da alƙibilar haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka a cikin shekaru biyar masu zuwa.”
Shugaba Buhari zai samu rakiyar uwargidansa Aisha da ministocin da suka haɗa da na harkokin waje Geoffrey Onyeama da na Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da Ministan babban birnin tarayya Abuja Mohammed Bello da na Lafiya Osagie Ehanire sai na Noma Mohammed Abubakar da na Masana’antu Ciniki da Zuba Jari Adeniyi Adebayo.
Sauran sun haɗa da, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da babban Daraktan hukumar leƙen asiri ta ƙasa Ambasada Ahmed Rufa’i.
Kamfanin dillancin labarai ƙasa NAN ya ruwaito cewa, ana sa ran mahalarta taron za su yi amfani da horaswar da za yi musu wajen inganta harkar shari’a da suka hada da ƙara haɗin gwiwa a fannin shari’a, da kuma alakar da ke tsakanin hukumomin shari’a da suka hada da horaswa da bada goyon baya, musamman a fannonin da suka shafi laifukan ta’addanci da kuma yarjejeniyar haɗin gwiwa ta tsaro da aikin haɗin gwiwa na horaswa kan yaƙi da aikata laifukan da suka shafi safarar muggan kwayoyi, da koyar da sana’o’in fasaha.
Ana sa ran taron zai amince da “Shirin Haɗin gwiwar haɗin gwiwar Turkiyya da Nahiyar Afirka daga shekarar 2021 zuwa 2026, wanda ya ƙunshi takamaiman ayyuka da Turkiyya da Tarayyar Afirka da ƙasashe membobinta za su aiwatar tare.
Haka kuma taron koli na uku zai haɗa da yin nazari kan haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka tun bayan taron ƙoli na biyu da kuma yin tsarin haɗin gwiwa a nan gaba.
NAN












































