Iyayen ɗalibai a jami’ar Maryam Abacha sun gudanar da zanga-zangar nuna ƙin amincewa da ƙaƙaba Naira Dubu Ɗari Bakwai da Hamsin a matsayin kuɗin kammala karatu da mahukuntan jami’ar suka yi

MAAUN New

Iyayen ɗalibai da masu kula da su a jami’ar Maryam Abacha da ke Kano sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da matakin jami’ar na ƙaƙaba kuɗin kammala karatu Naira Dubu Ɗari Bakwai da Hamsin ga ɗalibai.

Sun bayyana cewa adadin ya yi tsauri matuƙa, musamman ganin cewa taron karramawar yini guda ne kacal.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa takaddamar ta biyo bayan wasiƙar da ofishin mataimakin shugaban jami’a mai kula da rayuwar ɗalibai, Dr Hamza Garba, ya aika a ranar goma ga watan Nuwamba, wadda ta umurci dukkan ɗaliban da za su kammala tantance takardun su kafin ranar 30 ga Nuwamba.

Wannan umarni ya ƙara haifar da damuwa kan yiwuwar samun jinkiri ga fitar da sakamako da shirin bautar ƙasa.

Takardun da aka gani sun nuna yadda ake raba kuɗin, inda kudin taron karramawa ya kasance Naira Dubu Ɗari Biyu, kayan kammala karatu Naira Dubu Tamanin, masauki da sufuri Naira Dubu Ɗari, abinci da kayan sha naira Dubu Hamsin, daukar hoto da kayayyakin tunawa Naira Dubu Talatin, harkokin gudanarwa Naira dubu Ɗari Biyu da Arba’in, tare da ƙarin Naira Dubu Hamsin a matsayin kudin tanadi.

Wannan rabon kuɗi ya jawo ƙaruwar fushi daga iyaye da suka bayyana cewa babu wata hujja da ke tabbatar da wajabcin hakan.

Wasu daga cikin iyayen sun ce jami’ar ta saba ƙara kuɗaɗe ba tare da cikakkiyar hujja ba, musamman ganin cewa kudin karatu kansa yayi tsada, inda wasu fannoni ke biyan fiye da Naira Dubu Ɗari Takwas a zangon karatu daya.

Sun kuma yi tambaya kan dalilin saka kudin masauki da sufuri cikin abin da aka wajabta, duk da cewa ba kowane ɗalibi ko bako yake buƙatar irin wannan hidima ba.

Wata uwa, Hajia Hauwa Ibrahim Abdullahi, ta bayyana cewa iyaye sun buɗe dandali a Whatsapp na sadarwa domin tattaunawa kan lamarin, inda suka je jami’ar a makon da ya gabata domin jin bayani.

Ta ce sun gana da mataimakin shugaban jami’a mai kula da rayuwar ɗalibai, wanda ya ce umarnin ya fito ne daga shugabanci, sannan daga bisani aka kai su wurin shugaban jami’ar Farfesa “Dakta” Muhammad Israr, wanda ya tabbatar da hakan tare da alkawarin zai dawo da amsa cikin mako, amma har yanzu babu wani sauyi.

Halin damuwa ya yi ƙamari a tsakanin ɗalibai bayan jami’ar ta gargade su cewa rashin biyan kuɗin na iya kawo jinkiri ga tsarin sakamako da shigar su cikin bautar ƙasa.

Wasu ɗaliban suna ganin cewa haɗa mahimman matakan ilimi da kuɗaɗen karramawa ba daidai ba ne kuma tilastawa ne da bai dace da tsarin jami’a ba.

Iyayen dai suna kira ga hukumomin kula da ilimi da hukumomin gwamnati da su shiga tsakani wajen bincika wannan lamari, suna mai cewa abin da jami’ar ta yi ya saba da adalci ga iyalai da ke da wahalar tattalin arziki.

Sun buƙaci gudanar da tsarin da ya dace, fitar da bayanin gaskiyar kuɗin da ake kashewa, tare da sake duba adadin domin kauce wa ɗora nauyin da bai dace ba kan al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here