Pogba ya fara yi wa Juventus wasa a karon farko a bana

9fabcb90 b81a 11ed a974 074945f65d9d
9fabcb90 b81a 11ed a974 074945f65d9d

Paul Pogba ya fara buga wa Juventus wasa a karon farko ranar Talata, bayan da ya shiga karawar da ta doke Torino.

Juventus ta ci Torino 4-2 a wasan mako na 24 a gasar Serie A da suka fafata a Turin.

Dan kwallo tawagar Faransa ya shiga wasan na hamayya na ‘yan birnin Turin a minti na 68, wanda ya canji Enzo Barrenechea a lokacin suna 2-2.

Minti uku tsakani Bremer ya ci wa Juventus kwallo na uku.

Babban wasa na karshe da Pogba ya yi shine a Manchester United a Premier League a cikin Afirilun 2022, ya ji rauni tun kan hutu a wasan da Liverpool ta ci 4-0 a bara.

Ya sake komawa Juventus tun kan fara kakar bana, amma ya ji rauni a watan Yulin 2022.

Bayan da Pogba ya koma Juventus, magoya baya sun yi farin ciki da fatan zai mayar da kungiyar kan ganiya kamar yadda ya yi a baya.

Ya taka leda a Juventus tsakanin 2012 zuwa 2016 a matashin dan kwallo daga United da cin kofi hudu.

Tun farko bai yadda an yi masa tiyata ba, saboda zuwa gasar kofin duniya a Qatar, daga baya ya canja shawara da ta kai Faransa ba ta gayyace shi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here