Ganduje ya taya Tinubu murnar lashe zaɓe

334316534 1548143145763004 475231745474801528 n
334316534 1548143145763004 475231745474801528 n

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kwatanta zababben shugaban Najeriya da aka zaɓa Bola Tinubu a matsayin ɗan kishin dimokuraɗiyya.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne yayin taya Tinubu murnar lashe zaɓen shugaban Najeriya da ya yi a aɓen ranar 25 ga watan Febrairu.

A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaru ga gwamnan Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya yaba da irin jajircewar Tinubu da kuma na sauran mutane da suka tsaya wajen ganin sun cimma nasara.

“Bola Ahmed Tinubu jajirtaccen mutum ne da ke son ci gaban ƙasa da kuma al’umma saboda irin ayyuka da ya yi a faɗin ƙasa,” in ji Gwamnan.

Ganduje ya ce jajircewar da Tinubu ya yi na tsawon shekaru wajen ganin tabbatuwar dimokuraɗiyya a Najeriya, shi ya sa suka ga ya dace ya mulki ƙasar nan.

Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai yi aiki tukuru waje ganin ya shawo kan matsaloli da ƙasar ke fuskanta.

Gwamna Ganduje ya gode wa mambobin jam’iyyarsu da kuma dukkan waɗanda suka jajirce wajen samun nasararsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here