Rikici tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu, ya dauki sabon salo a ranar litinin, bayan matakin da gwamnan ya dauka na hana mataimakinsa shiga gidan gwamnati.
Shaibu ya samu kaduwa a lokacin da ya isa ofishinsa a ranar litinin, ya tarar da kofar ofishin da babbar kofar shiga a kulle.
An rawaito cewa mataimakin gwamnan ya yi kokarin kiran gwamnan domin jin dalilin rufe masa kofa, amma abin yaci tura.