Sanata daga Najeriya ya rasu a Birtaniya

Senate 1 750x430 (2)

Sanatan da ke wakiltar yankin Enugu ta Arewa Barrister Okey Ezea wanda ake kira Ideke, ya rasu a ranar Talata bayan ziyartarsa Birtaniya.

Marigayin ya rasu ne daidai lokacin da yake karɓar kulawar likitoci sakamakon jinya kafin rasuwarsa.

A cewar wani dattijo da ke da kusanci da shi, Chief Nkem Ossai, ya bayyana marigayi Ezea a matsayin mutum mai zuciya mai taushi wanda al’ummar mazabarsa za su yi kewarsa.

Ya bayyana cewa wannan rasuwa ta jefa yankin Nsukka da dukan Arewa ta Enugu cikin alhini, inda mazauna yankin da magoya bayan shi suka nuna mamaki kan rashin sa, musamman ganin cewa ya murmure gaba ɗaya daga wani matsalar hawan jini a watanni uku da suka gabata.

Ya ce yanzu haka yanayin da ake ciki a Nsukka ya cika da bakin ciki saboda mutuwar wanda ya yi alkawarin inganta yankin Arewa ta Enugu da maido mata ci gaba.

Rasuwar Sanata Okey Ezea babban gibi ne ga siyasar Jihar Enugu, kuma ayyukansa za su kasance abin tunawa ga mutane da dama.

Sanata Ezea shi ne dan majalisa na ƙarshe da ya rage a jam’iyyar Labour Party daga Jihar Enugu, domin sauran ‘yan majalisar jihar sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here