Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar (PDP) daga gudanar da babban taron ta ƙasa na shekarar 2025 da aka tsara yi a birnin Ibadan na jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Wannan umarni ne karo na biyu cikin makonni biyu da kotu ke dakatar da jam’iyyar daga shirinta na gudanar da taron.
Mai shari’a Peter Odo Lifu ne ya bayar da sabon umarnin a ranar Talata, inda ya hana jam’iyyar PDP ci gaba da shirye-shiryen taron, tare da hana hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) sa ido ko amincewa da sakamakon taron da aka shirya gudanarwa.
Umarnin kotun ya biyo bayan ƙarar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu kafa jam’iyyar, ya shigar, inda ya zargi PDP da ƙin ba shi damar siyan fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar, abin da ya hana shi shiga zaɓen cikin gaskiya.
Mai shari’a Lifu ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta gaza bin ka’idojin doka wajen shirya taron, musamman batun wallafa jadawalin taron domin sanar da mambobinta kamar yadda doka ta tanada.
Kotun ta ce la’akari da hujjojin da aka gabatar, Lamido ne zai fi fuskantar hasarar siyasa idan aka hana shi shiga tsarin, don haka dole ne a tsaya bisa adalci da bin doka domin kare tsarin dimokuraɗiyya.
Sakamakon haka, kotun ta haramta wa PDP ci gaba da gudanar da shirin taron a Ibadan ko wani wuri daban, tare da hana hukumar INEC saka idanu, gudanar da aikin lura, ko amincewa da duk wani sakamako da zai fito daga taron.
A baya, mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya ma ya bayar da irin wannan umarni a ranar 31 ga watan Oktoba, inda ya bayyana cewa shirye-shiryen PDP na gudanar da taron gangamin ƙasa sun sabawa tanade-tanaden doka.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ta kasa gudanar da sahihan tarurrukan jihohi a wasu sassan ƙasar, sannan wasiƙun taro da ke fita daga ofishin shugabancin jam’iyyar ana sa hannun shugaban ƙasaɗaya ba tare da na sakatare na ƙasa ba, abin da ke sa wasiƙun su zama ba bisa ƙa’ida ba.
Mai shari’a Omotosho ya ƙara da cewa PDP ta karya dokar da ke buƙatar sanar da hukumar INEC cikin kwanaki 21 kafin gudanar da tarurrukan jihohi da na ƙasa, abin da ya sanya taron da ake shirin yi cikin haɗari.
Saboda haka, kotun ta hana hukumar INEC karɓa, wallafawa ko amincewa da duk wani sakamakon taron da PDP ke shirin gudanarwa a Ibadan har sai jam’iyyar ta bi dukkan matakan doka yadda ya kamata.













































