Kimanin mutane 8 ne aka ruwaito sun mutu bayan murkushe su a filin wasa na Olembe da ya karbi bakuncin wasan Kamaru da Comoros a Yaounde babban birnin kasar Kamaru a gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar Litinin.
Wani faifan bidiyo da ya bayyana a yanar gizo, ya nuna yadda masu sha’awar kwallon kafa ke fafitikar samun damar shiga filin wasan.
Har ila yau, wani gidan talabijin na Kamaru, CRTV, ya ba da rahoton “fiye da rabin dozin din mutane sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata”.
Wata sanarwa da hukumar kwallon kafar Afirka ta fitar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
Sanarwar ta ce, “CAF tana sane da lamarin da ya faru a filin wasa na Olembe yayin wasan gasar cin kofin Afrika tsakanin Kamaru da Comoros a daren yau, 24 ga Janairu, 2022.
“CAF a halin yanzu tana binciken lamarin kuma tana ƙoƙarin samun ƙarin cikakkun bayanai kan abin da ya faru. Muna ci gaba da tuntuɓar gwamnatin Kamaru da kuma Kwamitin Gudanarwa na cikin gida.
“A daren yau, Shugaban CAF Dr Patrice Motsepe ya aika da Babban Sakatare, Veron Mosengo-Omba don ziyarci magoya bayansa a asibiti a Yaoundé.”













































