Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau I. Jibrin ya bayyana labarin dake yawo a wasu kafafen yada labarai cewa ya gana da Abdulaziz Ganduje, dan Gwamna Abdullahi Ganduje a matsayin labarin karya.
Solacebase ta tuna cewa a karshen makon da ya gabata ne kafafen sada zumunta da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suka yi kaca-kaca da labarin ganawar da Abdulaziz Ganduje da Sanata Barau Jibrin tare da yin rade-radin cewa an yi ganawar ne domin neman Sanata Barau ya janye takarar gwamna da yake yi.
Labarin ya nuna cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya aika dansa ya gana da Barau Jibrin don ya tsaya takarar Sanata a 2023 maimakon kujerar Gwamna.
Solacebase ta rahoto cewa Barau Jibrin mamba ne a bangaren G7 ta jam’iyyar APC a Kano dake adawa da gwaman Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Bangaren dai ya yi ta fafatawa da Gwamna Abdullahi Ganduje kan harkokin jam’iyyar, wanda har maganar ta kai ga Kotu.
Da yake magana da Solacebase a ranar Litinin, Sanata Barau Jibrin ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Hon. Shittu Madaki Kunchi ya musanta labarin, inda ya ce an dauki hoton ne a karshen shekarar 2020.
‘’Labarin ba gaskiya ba ne, domin wannan hoton ya kasance ne a ziyarar da Abdulaziz Ganduje ya kai ofishin Sanata Barau a majalisar tarayya a karshen shekarar 2020. Akwai ma dan majalisar wakilai ta Dambatta, Hon. Badamasi Ayuba,” in ji mai taimaka wa kafafen yada labarai.
Shittu Madaki Kunchi ya ce Barau Jibrin wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi bai ko je Kano a karshen mako kamar yadda labarin karya ya bayyana.
Mataimakin na Sanata Barau kan yada labarai ya bukaci al’umma da su daina yada irin wannan labari, inda ya bayyana cewa masu kirkirar labarin suna yi ne domin haifar da rudani a cikin al’umma.











































